Tun ranar talata rundunar da ke yaki da fashi da makami ta SARS, ta cafke Mista Samuel a kan wani labari da ya wallafa kan hana sanatoci shiga zauran majalisar dokokin da ke Abuja.
A cikin labarin nasa wanda wasu kafafan yadda labaran suka dauka, dan jaridar ya fallasa wata wasika da hukumar 'yan sanda ta aike wa Mukaddashin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo.
Wasikar mai dauke da shafi biyar, ta bayyana yadda tsohon shugaban hukumar DSS Lawal Musa Daura ya umarci jami'ansa su datse majalisa ba tare da neman izinin fadar gwamnati ba.
Hakazalika Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris ya nesanta kansa da abin da ya faru tare da bayyana cewa Lawal Daura ya yi gaban kasan ne a bisa son zuciya irin ta Siyasa.
Wasikar ta kuma bayyana inda ake tsare da Lawal Daura a wani katafaren gida da ke birnin Abuja.
Da kuma bayanan irin matakan da ake dauka da binciker na'urori da kamfutocin da jami'an hukumar DSS ke amfani da su wajen musayar bayanai.
Wani editan a Jaridar ta Premium Times, Muhammad Lere, ya shaida wa BBC cewa Jami'an SARS sun ce sun kama dan jaridar ne a bisa umarnin babban sufeto janar na 'yansandan kasar.
Muhammad Lere ya kuma ce kafin a cafke dan jaridar sai da aka soma tsare wata ma'aikaciyarsu mai suna Azeezat Adedigba da Babban Editan Jaridar Musikilu Mojeed, amma daga baya aka sake su.
'Yan sandan dai sun bukaci ala tilas Mista Ogundipe ya bayyana inda ya samo labarinsa, wanda yin haka ya saba wa ka'idar aikin jarida, in ji Muhammad Lere.
Premium Times ta kuma shaida mana yadda wani mataimakin kwamishina a hedikwatar hukumar 'yan sanda da ke Abuja, DCP Sani Ahmadu ke cewa babu wanda ya fi karfin doka ta hau kan sa.
'Ya ce bai damu Najeriya ta ji kunya ba, idan har tilasta wa dan jarida ya fadi inda ya samu bayanan sa ne, hakan bai zai hana shi ba.'
Tun a jiya laraba Kungiyar 'yan jaridu ta kasa, NUJ da Amnesty International da kungiyoyin fararen hula da kuma daidaikun mutane su nemi a sakin dan jaridar ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.
Amnesty ta yi tir da abin da ta kira tauye 'yanci albarkancin baki da matsi ga 'yancin aikin jarida a Najeriya.
A ranar Alhamis ma 'yan jarida sun gudanar da zanga-zangar neman a sako dan jaridan a hedikwatar 'yan sandan Najeriya.



Post a Comment
Post a Comment