'Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da garkuwa da gawar wata tsohuwa a kudu maso-gabashin Najeriya.
'Yan sanda daga Oweri, babban birnin jihar Imo, sun ce mutanen sun sace gawar ne daga wajen ajiye gawa a wani asibiti, kuma suka kai ta daji suna masu neman naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa daga asibiti da kuma iyalan marigayiyar, in ji 'yan sanda.
An kama wadanda ake zargin, wadanda a baya aka taba samu da laifi, a wani samamen da aka kai musu.
Kwanan nan aka sako mutanen daga gidan yari bayan sun yi zaman kaso bisa laifin garkuwa da mutane.



Post a Comment
Post a Comment