Inda take ikirarin zata iya yin komai saboda ta mallake yarima shi kuwa yarima babu wata mace da yafi tsana a rayuwarshi kamar Afrah yafi shiri da Farha saboda halayarta, Farha da Afrah yanxu haka suna jami'a ABU Zaria inda Farha take karatun law ita kuma Afrah yar mulkin tana karatun mass communication abun na Afrah yakara karfi lokacin da tashiga jami'a tahadu da wasu kawayenta Hauwaty(asalin Sunana ta Hauwa Ibrahim) da kuma Sofie (Safiya Al hassan Naira) mahaifan Sofie da Hauwaty abokanan juna ne mutane masu mutunci da sanin yakamata amma yayansu sam basu biyo halin su ba Farha batason kawancen dake tsakanin twin sister dinta da su kawayen nata, abokiyar Farha daya BALKISU wanda Afrah take gamin kamar zubda class ne wannan.
CIGABAN LABARI
Balkisu ce ta shiga part din yarima don takai mishi abinci tasani sarai cewa dokar shi ce duk wanda yakawo mashi abinci dole sai shi zai tsaya ya zuba mishi yaci kuma ya tsaya idan ya gama ya tattara, to yanzu ma hakan tayi saboda ta duba gurine ta zauna saboda ta jirashi yashigo, tana nan zaune taji alamun bade kofar side din ta mike zumbur saboda kada yasa me ta zaune, ko kallon inda take baiyi ba ya wuce straight to his bedroom don yayi wanka.
40 min latter
Yafito cikin shigar shi wace ya sa ta kananan kaya yayi kyau amma as usual fuskar nan a tamke take ba fara'a, shikam wannan ina tausayama rayuwarshi kullum mutum kamar an mishi bushara da mutuwa(Balkisu ce ke wannan zancen cikin ranta) ke xubamin abinci kin wani tsare ni da idanu sai alokacin ta san cewa yakara so gurin dinning table din ta sunkuyar da kai don a gaskiya taji kunya da ya ganta tana kallon shi saboda kota fada mishi abunda take tunani ba yarda zaiyi ba tana cikin xuba mishi abinci kwatsam sai ga Afrah bako sallamah tafado musu yarima yayi kamar bai gantaba yacigaba da sana'ar tashi wato danna waya to itama dai Balkisun bata cemata komai ba don tasan bazata tanka ba sai dai ta zageta kawai sai cewa tayi ke ki ajiye ki wuce zan cigaba harzata aje suka tsinkayi muryar yarima yana cewa kicigaba da aikin ki don ba ita tasa kiba balle ta hanaki(duk wannan maganar dayakeyi kanshi yana kan wayar shi) Afrah taji haushi sosai da ya dixgata agaban yar aiki amma haka ta danne tace haha Yaya Aryan zanfa samaka da kai na haryanzu bai daina abunda yakeba yace nasakine? Nan taja bakinta tayi shiru don tasan ba karamin akin shine yace tafita taba shi guri ba, saita ja kujera ta xauna kusada shi tana wani murmushi, Balkisu tagama serving dinshi taja da baya tayi tsaye tace ranka yadade angama sai alokacin ya dago ya kaleta yace ok, yafara cin abincin kenan Afrah ta dago tace ma Balkisu ai sai ki fita kibani guri inaso zanyi magana da yarima har zata bar gurin yace waya baki izinin tafiya take ta tsaya Afrah ta ce amma Yaya yadaga mata hannu yace idan abun mai muhimmanci ne sai kifadi anan koh, sai da ta kalli Balkisu ta zabga mata harara sannan tace dama nazone ingayyace ka birthday party dina wanda xanyi tomorrow yayi shiru kaman bai jita ba tace Yaya Aryan pls ππΌππΌππΌ yace keda Farha zakuyi ko kuma ke kadai sai da ta ya mutse fuska tace baza tayi ba yace dats my sis tace zakaxo yace sai na duba and pls no more words kaina yafara ciwo sannan ya kalli Balkisu yayi mata alama da ta dauke kayan ya gama ta dauke tsaf har zata fita ya daga muryar yace in kin ajiye ki dawo tace toh sannan ta fita itama Afrah tabi ta.
Shikuwa yarima tashi yayi yakoma palourn ya xyauna yana jiran zuwan Balkisu,bayan ta ajiye ta dawo ne ya kalleta yace zauna ta zauna ta dukar da kanta kasa yace kishirya gobe 4:30 zaki rakani bufday din Afrah ta dago zatayi magana ya daga mata hannu karki damu zangaya ma the only inaso kiyi shiga ta mutunci kina jina tace Insha Allah ya kalleta yace zaki iya tafiya kuma ki tabbatar da bawan da yashigo yadameni tace toh tafiya tayi ta sanar da masu tsaron gefen shi takara jaddada musu dannan ta wuce gurin uwar dakin ta...



Post a Comment
Post a Comment