input license here

Bamu Nemi Mbappe!!


Pep Guardiola ya sanar da cewa Manchester City bata bukatar siyan dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa wato Kylian Mbappe, mai shekara 20 a duniya.

Da yawan jaridun Birtaniya sun kawo wannan rahoton a yayin Kalamansa na fara wasannin zakarun turai na bana, ya ce ba gaskiya bane sun saka kudi har fam miliyan 200 don kawo dan gaban Faransan.

A kwanakin baya dai an jiwo Guardiola yana yabon dan wasan inda ya bayyana cewa nan gaba kadan dan wasan shine wanda tauraruwarsa zata haska kamar ta Ronaldo da Messi.

“Bana Magana akan dan wasan da bana kungiya taba hakan yasa koda yaushe nake kaucewa maganar canjin sheka ta ‘yan wasa saboda bai kamata kayi Magana akan dan wasan da bana kungiyarka ba” in ji Guardiola

Yaci gaba da cewa Mbappe babban dan wasa ne wanda kowacce kungiya take sha’awa amma kuma “kura tasan gidan mai babbar sanda” saboda kungiyar dayake bugawa wasa bazata yarda ta siyar dashi ba.

A karshe Guardiola ya bayyana cewa nan gaba yanason ganin Mbappe a kungiyar da yake bugawa wasa saboda matashin dan wasa ne wanda zai dade yana buga wasa batare daya gaji da wuri ba.
Related Posts
LastNg
Yusuf Musa By Name Iam the CEO/Founder Of www.lastng.com
SHARE

Related Posts

Subscribe to get free updates

Post a Comment

Copyright 2020 © ModernTheme

DMCA.com Protection Status