Rahotanni sun bayyana cewa tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane, yafara koyan turanci wanda hakan yasa wasu kungiyoyi da dama daga cikin kasar Ingila cikin shiri.
Kawo yanzu dai babu wani mai koyarwa wanda yakai Zidane tsada a duniya bayan yaja ragamar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar cin kofin zakarun turai guda uku a jere kafin yabar kungiyar a karshen kakar data gabata.
Zidane dai har yanzu bai karbi kowacce kungiya ba har yanzu sai dai rahotanni sun bayyana cewa yana jiran yaga ko Manchester United zata kori mai koyarwarta, Jose Mourinho daga aiki.
An bayyana cewa Zidane tuni yafara nuna alamun yakusa dawowa domin cigaba da koyarwa bayan ya fara koyan turanci kuma ana ganin Manchester United itace kungiyar da kawo yanzu zata iya bashi aiki.
Kwanakin baya dai an hango Zidane tare da matarsa a tsakiyar birnin Landan kuma a kwanakin baya an danganta shi da komawa kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kasar Faransa kafin kuma su dauki mai koyarwa.



Post a Comment
Post a Comment